An sake gano ƴan matan Chibok biyu a Jihar Borno

0
98

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa ta ƙara ceto ƴan matan Chibok guda biyu a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Babban kwamandan Operation Hadin Kai Manjo Janar Christopher Musa ne ya tabbatar da hakan inda ya ce irin matsin lambar da ƴan Boko Haram ɗin ke fuskanta ne ke sawa suna guduwa suna barin ƴan matan Chibok ɗin.

Manjo Janar Musa ya shaida wa BBC cewa ɗaya daga cikin matan da aka ceto an same ta ne a ranar 29 ga watan Satumba inda aka same ta da yara huɗu.

Yana Pogu, ita ce ta 19 a jerin ƴan matan na Chibok da aka yi garkuwa da su.

Ya ce akwai maza biyu da kuma ƴan biyu mata da ta haifa inda ya ce ƴan biyun jarirai ne sabuwar haihuwa.

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa ta ƙara ceto ƴan matan Chibok guda biyu a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Babban kwamandan Operation Hadin Kai Manjo Janar Christopher Musa ne ya tabbatar da hakan inda ya ce irin matsin lambar da ƴan Boko Haram ɗin ke fuskanta ne ke sawa suna guduwa suna barin ƴan matan Chibok ɗin.

Ya bayyana cewa dakarun Birged na 21 ne suka gano ta a samamen da suka kai a yankin ƙauyen na Mairari da ke Ƙaramar Hukumar Bama.

Sa’annan a ranar 2 ga watan Oktoba, an gano Rejoice Sanki wadda sunanta ne na 70 a jerin yan matan na Chibok da aka yi garkuwa da su.

Ita kuma an gano ta ne yankin Kawuri da ke Ƙaramar Hukumar Konduga tare da ƴayanta biyu.

Kwamandan ya tabbatar da cewa a bana 2022 kawai, an samu nasarar ceto ƴan matan Chibok 11.

Tun a 2014 ne dai ƴan Boko Haram suka sace ƴan mata a makarantar gwamnati ta mata da ke Chibok inda suka kwashe mata 276.