Ku shirya wa matsananciyar yunwa a Arewa – Sarkin Zazzau

0
97

Sakamakon ambaliyar ruwan da ya addabi sassan arewacin Najeriya tare da ayyukan ‘yan bindigar da suka hana noma a yankin, Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamali ya gargadi shugabannin yankin da su tashi tsaye domin tunkarar matsalar yunwa mai tsananin dake yiwa kasar barazana.

Bamali yace mutanen yankin basa bukatar wani masanin da zai shaida musu cewar an kama hanyar karancin abincin da kuma yunwa sakamakon wadannan matsaloli guda biyu da suka hana jama’a gudanar da harkokin su na noma wanda shine babban sana’ar da aka sansu da shi.

Sarkin yace duk da yake suna ci gaba da addu’a domin Allah ya kawowa jama’a dauki, ya zama wajibi a fadakar da mutane da su tashi tsaye domin samun madogara saboda ganin girmar matsalar.

Basaraken yace lokaci yayi da jama’ar yankin zasu tashi daga baccin da suke yi domin sake dabaru ganin yadda a shekaru 2 da suka gabata, yankin yayi fama da wadanan tagwayen matsaloli a jere.

Sarkin ya kuma janyo hankalin jama’ar yankin cewar a halin da duniya take ciki a yau, babu wani yanki na duniya da ake bada ilimi kyauta, saboda haka ya dace jama’a su zage damtse wajen tallafawa bangaren ilimi, duk da yake yace baya bukatar ganin an tsawwalawa jama’a kudin makarantar.