Gwamnatin jihar Anambra ta bayar da umarnin garkame gidajen Caca

0
94

Gwamnatin Jihar Anambra ta bayar da umarnin rufe dukkan cibiyoyin caca a jihar.

BBC ta rawaito cewar, umarnin ya biyo bayan zargin aikata zamba da kuma wadansu munanan ayyuka a cibiyoyin da ake caca.

Jaridar Punch ta ce kwamishinan al’adu na jihar, Donatus Onyenji da shugaban hukumar haraji Richard Madiebo da kuma kwamishinan yada labarai Chikodi Angra ne suka fitar da sanarwar.

Sun ce gwamnati ta samu korafe-korafe game da ayyukan masu caca wadanda ake zarginsu da yin coge da kuma cuwa-cuwa.

Jami’an sun ce gwamnatin Chukwuma Soludo a Jihar Anambra ba za ta lamuncin wannan abu ba.