An cafke ma’aikatan da suke katin dan kasa na bogi

0
84

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa dakarunta tare da hadin gwiwar hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya NIS da rundunar ‘yansandan Nijeriya sun cafke wasu jami’an bogi biyu na hukumar ba da shaida katin dan kasa a Jamhuriyar Nijar.

Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo-Janar Musa Danmadami, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a taron mako biyu kan ayyukan sojojin Nijeriya tsakanin 6 zuwa 20 ga Oktoba, 2022 a hedikwatar tsaro da ke Abuja ranar Alhamis.

Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke Gagamari a Jamhuriyar Nijar a lokacin da suke yi wa wadanda ba ‘yan Nijeriya rijista ba tare da sanya su cikin ma’adanar bayanai ta Nijeriya ba.

Danmadami ya zayyana kayayyakin da jami’an tsaro suka kwato daga hannun wadanda ake zargin da suka hada da: Na’urar rajista ta kasa (NIN), na’urar buga kati, na’urar bin diddigin kwamfuta da injin janareta da dai sauransu.

“A ranar 13 ga Oktoba, 2022, sojoji tare da rundunar ‘yansandan Nijeriya da jami’an NIS sun kama wasu jami’an hukumar kula da bayanan sirri na kasa (NIMC) guda 2 da ake zargin na bogi ne.

“An bayyana cewa wadanda ake zargin sun ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira na Gagamari da ke Jamhuriyar Nijar ne domin yin rijistar wadanda ba ‘yan Nijeriya ba a sansanin ‘yan gudun hijirar.

“Kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da na’urar rijista ta kasa (NIN), na’urar buga kati, na’urar bin diddigin kwamfuta da injin janareta da dai sauransu.”

Da yake tsokaci game da ci gaban yayin gabatar da tambayoyi daga ‘yan jarida, tsohon Daraktan DMO, Manjo-Janar Benard Onyeuko, ya ce za a bankado aniyar jami’an bogi idan an kammala bincike.

Ya ce wannan wani sabon abu ne da sojoji suka samu don haka ya kamata a yaba wa rundunar soji.

“Rundunar sojin ta cancanci a yaba mata bisa nasarar da ta samu wajen kame wadannan masu laifi a kasar waje.”