Zan kammala aikin wutar mambila idan aka zabe ni – Tinubu

0
106

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin kammala aikin wutar lantarki na Mambila da gwamnatin Buhari ta ce tana aiki a kan sa.

Tinubu ya kuma yi alkawarin shawo kan matsaloli da arewacin Nijeriya ke fuskanta da kuma kasar baki daya da zarar ya zama shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a wani taro da kungiyoyi masu fada aji na arewacin Nijeriya suka hada da kungiyar dattawan Arewa suka shirya wa ‘yan takarar shugaban kasa a JIhar Kaduna.

Tinubu ya ce cikin abubuwan da zai fara yi shi ne kammala aikin wutar Mambilla da aka shafe tsawon shekaru ba tare da yin aikin ba, inda ya ce tashar za ta samar wa da kasar wuta mai karfin megawatt 3,050 wanda kuma zai kasance daya daga cikin tasha mafi girma a fadin kasar.

“Abin da yake kawo jinkirin kammala wannan aikin shi ne rashin isassun kudade. Ba a ware isassun kudade ga manyan ayyuka masu daukar dogon lokaci. Za mu kammala wadannan aiki saboda muna zuwa da wani tsari mai kyau ga kasar nan,” in ji Tinubu.

Ya kuma ce zai kawo masu zuba jari a ciki da kuma wajen kasar wadanda za su kammala aikin da zai kawo wa kasar ci gaba.