Madagascar ta kori ministanta saboda goyon bayan Ukraine

0
96

Shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina ya kori ministan harkokin wajen kasar Richard Randriamandranto, ba tare da bayar da wani bayani ba.

Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da Madagaskar ta kada kuri’ar Allah wadai a majalisar dinkin duniya, kan mamayar da Rasha ta yi a Ukraine.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai shugaban kasar ya rattaba hannu a kan matakin da ya dauka na korar ministan nasa kafin ya yi balaguro zuwa Morocco.

Dangane da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, Madagascar ta dauki matakin ne, duk da gayyatar da Tarayyar Turai da Amurka suka yi mata kan ta yi tir da mamayar Rasha.

Amma a ranar 12 ga Oktoba, Madagascar, tare da wasu kasashe 142, suka yi Allah wadai da “mamayar da Rasha ta yi ba bisa ka’ida ba” a Ukraine, sabanin matakin da kasar ta dauka tun farkon yakin.

A ranar Asabar, tashar TVM ta yada rahotannin da ke zargin ministan harkokin wajen kasar da daukar wannan mataki ba tare da tuntubar shugaban kasa ko kuma firaminista ba.

Kafar yada labaran Malagasy ce ta ba da labarin a ranar Litinin, inda ta zargi ministan da rashin biyayya ga fadar shugabancin kasar.

A ranar Talata ne bayan bayyana a zauren majalisar dokokin kasar, Richard Randriamandranto ya ki amsa tambayoyin manema labarai, yana mai cewa “ba za mu haifar da wata baraka ba.

Ga bangaren ‘yan adawa kuwa, babban jami’in jam’iyyar HVM na kasar, Rivo Rakotovao, y ace ministan “ya taka rawar gani kawai don gyara kuskuren diflomasiyya ne”.