Kwanturolan Kwastam Ayalogu, ya yanke jiki ya mutu a filin jirgi a Kano

0
81

Kwantorola mai kula da Kasuwanci na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Anthony Ayalogu, ya rasu yana tsaka da aiki a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.

Ajali ya riski Kwanturola Anthony Ayalogu ne bayan ya yanke jiki ya fadi magashiyyan, sakamakon kamuwa da rashin lafiya, jim kadan bayan saukarsa a filin jirgin domin gudanar da aiki.

Hukumar ta ce, nan take aka garzaya da shi Asibitin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, amma, “Duk kokarin da likitoci suka yi na farfado da shi ya gagara, inda da misalin karfe 8.20 na dare ranar 17 ga Oktoba, 2022, aka sanar cewa ya rasu.

“Ya kwanta dama yana da shekara 57 a Asibitin Runduna ta 465 ta Sojin ta Najeriya da ke Kano.”

Sanarwar da sashen yada labaran hukumar kwastam din ya fitar ta hannun AA Maiwada, ta ce, Shugaban Hukumar na kasa, Hameed Ali, ya jajanta wa iyalan mamacin, yana mai cewa Najeriya ta yi babban rashin hazikin jami’i.

Kwanturola Anthony Ayalogu, dan asalin Karamar Hukumar Onitsha ta Arewa ne a Jihar Anambra State, kuma ya fara aikin kwastam ne a ranar 24 ga Satumba, 1991, a matsayin Mataimakin Karamin Hafsa (CAS).

AMINIYA