Kuraye na cin gawarwakin waɗanda suka mutu a yaƙi a kasar Habasha

0
98

Kuraye suna cika cikkunansu da naman gawarwakin mutanen ƙauye, ana yi wa garuruwa da birane ruwan wuta ta sama, an tursasa wa tsofaffi da ƴan mata shiga aikin soja duk waɗannan na daga cikin munanan labaran da ke fitowa daga yaƙin basasar Habasha, wanda ya yi sanadiyyar rayukan dubban ɗaruruwan mutane a yankin ƙasar na Tigray mai ɗinbin tarihi.

A baya yankin ya kasance mai jan ra’ayin masu yawon buɗe ido, inda masu zuwa yankin kan ziyarci mujami’u da aka sassaƙa a cikin dutse, da wuraren tarihi na musulunci da kuma tsoffin litattafan da aka rubuta da harshen Ge’ez.

A cikin shekaru biyu da suka gabata, nasara ta rinƙa sauya hannu tsakanin ɓangarorin biyu da ke yaƙi da juna a yankin.

Yanzu Tigray ya zama fagen daga, inda gamayyar dakarun Ethiopia da na Eritrea suke gwabza faɗa da na ƙungiyar masu rajin ƴanta al’ummar Tigray (TPLF), ana faɗa domin ƙwace iko da yankin wanda a baya ake wa kallon muhimmin ginshiƙi a siyasar Habasha – wanda a tarihi yake cikin yankin da ake kira Abyssinia.

An kwashe watanni 17 yankin na a kulle – babu bankuna, babu sadarwar waya, babu intanet, sannan kuma ba a iya samun kafafen yaɗa labarai.