‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da jami’an lafiya da marasa lafiya a jihar Neja

0
109

Akalla mutane biyu ne aka bindige har lahira yayin da aka yi garkuwa da da yawa a lokacin da ‘yan bindiga suka afkawa babban asibitin Abdulsalami Abubakar da ke Gulu a karamar hukumar Lapai a jihar Neja a daren ranar Litinin.

Ya zuwa yanzun, ba a tantance sunayen wadanda aka kashe ba, an tabbatar da cewa daga cikin wadanda aka sace akwai Babban Likitan jinya, likitan magunguna, ma’aikatan jinya da kuma marasa lafiya da masu jinyarsu.

Daily trust ta rahoto cewa, daga cikin ma’aikatan asibitin da aka sace akwai shugaban asibitin jinya Dr. John, shugaban sashen nazarin jini, Usman Zabbo, da ma’aikacin dakin gwaje-gwaje, Awaisu Bida.

Haka kuma an sace matar shugaban ma’aikatan jinya da ‘ya’yansa mata, matar da diyar babban likitan magunguna, da sauran ‘yan uwan ​​majinyatan.

An yi zargin cewa, harin an kai shine na musamman domin sace jami’an lafiya don su yi jinyar wasu ‘yan bindiga da suka jikkata a dajin yayin hare-haren da sojoji ke kai musu a dajin.

Wani ma’aikacin asibitin da ba ya bakin aiki a lokacin da aka kai harin ya bayyana ta wayar tarho cewa an yi garkuwa da marasa lafiya wadanda ciwon su bai yi tsanani ba.

Ya ce maharan da suka shafe sa’o’i suna ta harbe-harbe ba tare da wata barazana daga hukuma ba, ‘yan banga kuma sun tsere domin tsira da rayuwarsu.

Har yanzu ‘yan sanda ba su ce uffan ba, sai dai Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya yi alkawarin cewa zai dawo da cikakken bayani game da harin.