Sojoji sun cafke mutum 40 masu yi wa ‘yan ta’adda safarar kayan abinci

0
100

Rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Taskforce (MNJTF), ta ce sojojin hadin gwiwa na shiyya ta 3 da ke Monguno a ranar 11 ga Oktoba, 2022, sun cafke wasu mutane 40 da ke yi wa ‘yan ta’adda safarar kayan abinci.

A wata sanarwa da Kamarudeen Adegoke, Laftanar Kanal, Shugaban Ofishin Yada Labarai na Sojoji na Chadi, da ke N’Djamena, ya fitar a ranar Talata, ya ce an samu nasarar ne sakamakon wani samame da jami’an leken asiri suka gudanar a kan wata hanyar da ake zargi da kai kayan agaji.

Ya ce a yayin gudanar da samamen an gano buhunan wake 64, buhunan masara biyu, da sauran kayan abinci masu yawa, wadanda ake kai wa mabiyar ‘yan ta’addan.

Ya ce an kuma gano wasu buhunan wake 300 da buhunan masara 100 wanda suka lalace a wurin.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, a ranar 11 ga watan Oktoban 2022, dakarun bataliya ta 68 da ke sintiri tare da rundunar hadin gwiwa ta Civilian Joint Task Force (CJTF) tare da Mallam Fatori- Bandamari-Bari – Korarawon, sun gano tare da kwace buhunan kifi 12 da jakuna tara da ake zargin suna dauke da su.

Ana amfani da su wajen jigilar kayayyaki zuwa ga ‘yan ta’addan da ke boye a yankin tafkin Chadi.

A cewarsa, kwamandan rundunar ta MNJTF, Manjo-Janar Abdul Khalifah Ibrahim, ya yaba wa sojojin tare da bukatar su da su ci gaba da dagewa wajen katse duk wani abu da ake bai wa masu aikata laifuka domin tabbatar da samun cikakken zaman lafiya da tsaro a yankin tafkin Chadi.