Hadarin mota ya hallaka mutane 11 tare da jikkata 9 a Bauchi

0
92

Rahotanni daga jihar Bauchi dake Najeriya na cewa, akalla mutane 11 ne suka mutu yayin da wasu tara suka samu raunuka daban-daban a lokacin da wata motar tirela ta yi taho mugama da wata bas mai daukar mutane 18 a kauyen Hawan Jaki da ke Alkaleri kan hanyar Bauchi zuwa Gombe.

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Bauchi Yusuf Abdullahi wanda ya tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin a wannan Lahadin, ya ce hatsarin da ya auku ranar Asabar ya rutsa da motocin kasuwanci guda biyu da suka hada da wata motar Hiace na kamfanin Yankari Express mallakin gwamnatin jihar Bauchi da kuma tirelar kirar DAF mallakin rukunin kamfanonin Dangote.

Abdullahi ya bayyana cewa, tawagar ceto na hukumar FRSC ta garzaya wurin da lamarin ya faru jim kadan bayan samun rahoton inda aka kwashe su zuwa babban asibitin Alkaleri inda aka tabbatar da mutuwar tara daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kara da cewa, “wasu wadanda suka jikkata sun mutu daga baya.”

Kwamandan ya yi kira ga masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar da su kiyaye ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa tare da daina gudu da ya wuce kima musamman a cikin watannin ake yawaitar zirga-zirgar ababen hawa a manyan hanyoyin.