An rantsar da sabuwar gwamnati a jihar Ekiti

0
91

An rantsar da Sabon Gwamnan jihar Ekiti Abiodun Oyebanji

Wanda zai kama aiki gobe Litinin.

Babban Alkalin jihar Ekiti Oyewole Adeyeye shine ya rantse dashi a yau Lahadi .

Jaridar Hausa 24 ta rawaito cewa a ranar 21 ga watan Yunin 2022 hukumar zabe ta kasa INEC ta tabbatar da Abiodun Oyebanji na Jam’iyar APC a matsayin Wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar na ranar 20 ga watan Yunin

A yayin karbar rantsuwar kama aiki Sabon Gwamnan na Ekiti Abiodun Oyebanji yayi alkawarin kare mutucin Yan Ekiti da Kuma yin iya yinsa Dan kawo sauyi a jihar .

Daga cikin wadanda duka halarci taron rantsar da gwamnan akwai Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyar APC Bola Tinubu da gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu da na Plateau Simon Lalong da Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos da Badaru Abubakar na Jigawa da Godwin Obaseki na jihar Edo da Kuma gwamna Dapo Abiodun na Ogun