Sarkin Kano ya halarci bikin dawakai a kasar Morocco

0
97

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bar Najeriya zuwa kasar Maroko domin halartar bikin dawakai karo na 13 a birnin El-Jadida da ke gabar teku tsakanin 18 ga Oktoba zuwa 22 ga Oktoba, 2022.

Masu shirya bikin ne suka gayyaci sarkin a matsayin babban bako na musamman a yayin bikin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na masarautar, Abubakar Kofar-Naisa, ya fitar ranar Asabar.

Bikin doki yana É—aukar fa’idodin doki da yawa a cikin Noma, haÉ“akawa da adana abubuwan al’adu, muhalli, da wasanni kuma a matsayin tushen nishaÉ—i wanda ke haifar da alaÆ™ar zamantakewa mai Æ™arfi.

Tuni dai wata tawaga ta Kano ta je Masarautar domin halartar bukukuwa da gasa a yayin bikin.

Sarkin Aminu Ado Bayero ya samu rakiyar Alhaji Ahmad Ado Bayero, Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Amb. Ahmed Umar, Dan Malikin Kano, da Malam Isa Bayero, da sauran ma’aikatan Masarautar.