Dalibin likitancin da yazama dillalin abinci a lokacin yajin aikin ASUU ya rasu

0
98

Allah ya yi wa Usman Abubakar-Rimi, wanda ya zama mai sayar da abinci a lokacin yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU),  rasuwa.

Marigayin dalibin shekarar karshe ne a fannin likitanci da tiyata a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS).

Abubakar-Rimi ya bude gidan sayar da abinci a Unguwar Diflomasiyya dake Sokoto. Ya rasu ne a ranar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya.

Shugaban cibiyar ‘yan kasuwa na karni na 21, Umar Idris ne ya tabbatar wa NAN rasuwar a ranar Asabar.

Idris ya ce an yi jana’izar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garinsu da ke karamar hukumar Rimi a Katsina.

An bayyana Abubakar-Rimi a matsayin mutum mai tawali’u kuma kwararren dalibi kuma dan kasuwa.

A watan Satumba, marigayin ya shaida wa NAN cewa ya tsunduma harkar abinci ne saboda yajin aikin ASUU da aka dade ana yi.

Marigayin dalibin ya kuma tuna cewa ya yi amfani da kulle-kullen COVID-19 don fara kasuwancin rarraba kwai da kaza.