Matawalle ya ba da sanarwar rufe kananan hukumomin jihar Zamfara guda 3

0
88

A ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin Zamfara ta sanar da cewa za a kulle kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gummi, biyo bayan barkewar hare-haren ‘yan bindiga a kan al’umma.

Wannan matakin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Ibrahim Dosara ya fitar ranar Juma’a a Gusau.

“Gwamnati ta ba da sanarwar dakatar da wasu manyan garuruwa tara domin dakile yawaitar hare-haren da ake kai wa a yankunan da lamarin ya shafa.

“Garuruwan Yarkofoji, Birnin Tudu, Rini, Gora Namaye, Janbako, Faru, Kaya, Boko da Mada.

“Gwamnati ta kuma sanar da rufe kasuwannin Danjibga da Bagega da kuma Colony zuwa Lambar Boko Road, Bakura zuwa Lambar Damri da Mayanchi- Daki Takwas zuwa Gummi Road.“Sauran hanyar Daki Takwas zuwa Zuru, Kucheri-Bawaganga – Wanke Road, Magami zuwa Dangulbi Road da Gusau zuwa Magami Road.

“An dauki matakan ne domin saukaka kokarin jami’an tsaro wajen fatattakar masu aikata laifuka a yankunan,” in ji gwamnatin.

Gwamna Bello Matawalle ya kuma bayar da umarnin dakatar da duk wani taro da ayyukan jam’iyyar APC cikin gaggawa a wani bangare na kulawa da jajantawa gwamnatinsa ga al’ummar da abin ya shafa.

“Bugu da kari kuma, gwamnati ta dakatar da duk wasu harkokin siyasa a jihar har har sai an samu sanarwa.