‘Yan Najeriya miliyan 95 ne za su kada kuri’a a zaben 2023 – INEC

0
119

Wasu alkaluma da hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta fitar, sun nuna cewa ‘yan kasar akalla mutum miliyan 95 ne za su kada kuri’a a zabukan shekarar 2023 da za su gudana a kasar.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da ke bayyana hakan a jiya Laraba yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan tabbatar da gudanar da karbabbun zabuka a kasashe da ya gudana a birnin Washington na Amurka ya bada tabbacin shirye-shiryen hukumar da ya ke jagoranci na gudanar da sahihin zabe.

A cewar farfesa Yakubu yayinda jumullar kasashen yammacin Afrika 14 ke da yawan wadanda suka cancanci kada kuri’a miliyan 73, Najeriya da ke zama cikon ta 15, ne da yawan masu kada kuri’ar miliyan 95 ita kadai.

Wannan kididdiga ta zo ne a yayin da ya rage kasa da watanni biyar a gudanar da zaben shugabancin Najeriya a 2023, babban zabe na bakwai a jere tun bayan komawar kasar zuwa mulkin dimokaradiya a shekarar 1999.