Bamu da wani shiri na sayar da kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya – Gwamnati

0
96

Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Nijeriya ta ce ba ta da wani shiri na sayar da kamfanin rarraba wutar lantarki ta Nijeriya (TCN).

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, ma’aikatar ta bukaci jama’a da su yi watsi da kalamai dangane da wani zance da ba shi da tushe na mayar da kamfanin TCN mai zaman kansa a hannun ‘yan kasuwa.

Wannan martani ne ga rahotanni da maganganun da wasu kafofin yada labarai ke yi na cewa akwai wani shiri na mayar da TCN hannun ‘yan kasuwa.

Wasu daga cikin rahotannin sun yi ikirarin cewa za a fara zaman tattaunawa kan batun nan da wasu watanni masu zuwa.

“Wadannan rahotannin ba gaskiya ba ne, kage ne kawai da nufin yada fargaba a bangaren ma’aikatan wutar lantarki da ‘yan Nijeriya, sabida dakile shirin da kamfanin ke yi na wadata ‘yan Nijeriya da wutar lantarki”

“Gwamnatin tarayyar Nijeriya ba ta da niyyar sayarwa ko mayar da kamfanin wutar lantarki ta Njeriya a hannun ‘yan kasuwa, kuma babu wani a cikin Gwamnatin tarayya da ya bayyana aniyar sayar da TCN.” Inji gwamnatin tarayya