Kwanan nan za mu janye yajin aiki – ASUU

0
85

Kungiyar Malaman Jami’a ta Kasa (ASUU), ta ce nan ba da jimawa ba za su janye yajin aikin da suka yi wata takwas suna yi.

Da yake magana a tattauna da Majalisar Wakilai kan daidaita kungiyar da Gwamnatin Tarayya, Shugaban ASUU na Ƙasa, Farfesa Emmanuel Esodeke, ya ce bisa dukkan alamu, yajin aikin ya zo karshe.

“Muna kyautata zaton nan da ’yan kwanaki kalilan za a janye yajin aikin.
“Muna so a samar da kyakkyawan tsarin albashi ta yadda malamai daga ko’ina a fadin duniya za su rika kwadayin zuwa koyarwa a jami’o’in kasar nan,” in ji Farfesa Osodeke.

A lokacin ganawar tasu ranar Litinin da shugabannin Majalisar Wakilai a Abuja, Farfesa Emmanuel Esodeke ya ce daga abin da kungiyar ta gani a wurin taron, akwai alamun nasara.

Ya ce, “Muna fata a wannan karon ba za a samu wasu mutane ko kungiya da za su haifar da abubuwan da za su sa kungiyar ta shiga cikin wani mawuyacin hali ba.”

Ya kuma yi fatan shiga tsakani da shugabannin Majalisar suka yi shi ne na karshe saboda dalibai su koma aji.

Ya kara da cewa fafutukar ASUU tana yi ne domin ceto bangaren ilimi da jami’o’in kasar nan.

Ya ce ya kamata kuma a rika biyan jami’o’in Najeriya da kudi mai kauri domin jawo hankalin daliban kasashen waje, yayin da ya nuna damuwa kan wasu nagartattun malamai da ke barin kasar.

Ya ci gaba da cewa, “Muna godiya ga Shugaban Majalisar kan wannan shiga tsakani kuma dole ne mu hada kai domin kowane dan Najeriya ya yi alfahari da jami’o’inmu.”

Ya ce yajin aikin bai kamata ya wuce makonni biyu ba, “da majalisar dokokin kasar ta sa baki kafin yanzu.”

Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce tsoma bakin da shugabannin majalisar suka yi ya yi tasiri.