Abinda yasa muka kara kudin Data duk da gwamnatin Najeriya bata so – MTN da Airtel

0
87

Gwamnatin tarayya ta magantu akan Karin kudin Data da kamfanonin Sadarwa na MTN da Airtel sukayi a kasar Nan.

Kamfanonin guda biyu sunyi Karin kudin Data din ne da kaso 10 cikin dari .

Cikin wata wasika da suka aikewa da hukumar kula da harkokin Sadarwa ta kasa ,a lokuta daban daban kamfanonin Sadarwa na MTN da Airtel sunce ya zama wajibi su Kara kudin Sayan Data saboda Koma bayan tattalin arzikin kasa da Kuma nauye nauyen da suke kan kamfanonin ciki harda tsadar man Disal.

Saidai hukumar Kula da harkokin Sadarwa ta kasa NCC tace yayi wuri kamfanonin guda biyu su dauki wannan mataki ,sannan Kuma Dole akwai matakan da ake bi kafin kaiwa ayi Karin Data ko kudin Kiran waya Dana Tura Sako.

 

PUNCH.