Farfesa Folasade ta zama mace ta farko da ta samu ikon zama shugaban babbar jam’ia a Najeriya 

0
99

An nada Farfesa Folasade Ogunsola a matsayin mace ta farko da ta fara zama shugaban jami’ar Legas (UNILAG)

Ogunsola ta yi nasara ne cikin mutane bakwai da aka tantance sunayensu don nadin mukamin.

Daga cikin sauran mutanen da aka tantance akwai Akinyeye na Tsangayar Tarihi; Mathew Ilori da Adeyinka Adekunle na Sashin Nazirin Kananan Halitu da Tsirai; Imran Smith, Tsangayar Koyar da aikin shari’a; Timothy Mubi na Tsangayar Nazarin Gidaje Da Filaye da Ayo Olowe na Tsangayar Bangaren Kudi sai ita Folashade Ogunsola na Kwallejin Likitanci.