Kotun daukaka kara ta umarci ASUU da su koma bakin aiki cikin gaggawa

0
82

Kotun daukaka kara ta bayar da wannan umarni ne a yau yayin da take ba ASUU damar daukaka kara kan hukuncin da mai shari’a Polycarp Hamman na babbar kotun masana’antu ta kasa a Abuja ta yi a ranar 21 ga Satumba, 2022, inda ta bukaci mambobin kungiyar su koma bakin aiki.

Kotun da ke karkashin Mai shari’a Hamma Barka, ta yi gargadin cewa idan ASUU ta ki bin umarnin kotun, to nan take ta rasa ‘yancin daukaka kara kan hukuncin da karamar kotu ta yanke.

Sai dai kotun ta yi watsi da bukatar da ASUU ta yi na a dakatar da aiwatar da umarnin kotun masana’antu, bisa bukatar lauyan mai kara, Femi Falana (SAN) na janye bukatar.

Da yake karanta hukuncin jagoran kwamitin mutane uku, Mai Shari’a Hamma Barka, ya umarci ASUU da ta shigar da karar da ta  daukaka akan hukuncin da karamar kotun ta yanke a cikin kwanaki bakwai.