’Yan ta’adda sun sako fasinjojin jirigin kasa 23 da suka rage a hannunsu

0
107

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta sanar cewa ’yan bindiga sun sako fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna 23 da suka rage a hannunsu.

’Yan uwan fasinjojin jirgin sun tabbatar wa Aminiya cewa an sako ’yan uwansu kuma a halin yanzu sun samun kulawa a asibiti.

Tasiu Muhammad Barau ya shaida wa Aminiya cewa, “Na yi magana da dan uwana Abdullah, wanda guda ne daga fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna da aka yi garkuwa da su, kuma ya shaida min cewa yana samun kulawa a wani asibiti a Abuja.”

Shi ma wani dan uwansa, Aminu Usman wanda aka fi sani da Dan Nasarawa, ya ce an kira su an sanar da su cewa an sako dan uwansu da ke cikin fasinjojin jirgin kasan.

“An kira mu cewa an sako Aminu, yanzu muna jira ne mu ji lokacin da za a mika mana shi,” in ji shi.

Sai dai ya ce, ba zai iya cewa an kawo su Kaduna ba, ko suna Abuja, amma “Abin da ya fi mana muhimmanci shi ne an sako fasinjojin.”

Sanarwar da Kwamitin Babban Hafsan Tsaro kan ceto fasinjojin ya fitar ta ce a yammacin ranar Laraba aka mika fasinjojin ga kwamitin wanda Shugaban Kasa ya kafa karkashin kulawar Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor.

A ranar 28 ga watan Maris, 2022 ne ’yan ta’addan Boko Haram suka kai harin bom kan jirgin kasan da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja inda suka kashe akalla mutum tara, suka yi awon gaba da wasu kimanin 60.