’Yan bindiga sun kashe mutum 12 a Taraba

0
87

Wasu ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 12 a kauyen Mubizen na Karamar Hukumar Bali da ke Jihar Taraba.

Ardo Umar Bello, wanda shi ne shugaban kungiyar Dandalin Makiyaya na Jihar Taraba, ya tabbatar da cewa ’yan bindigar sun je garin ne sanye da kakin bijilanti.

Ya ce sun tara mutane a wani waje inda suka gaya musu cewa sun je domin su kama wasu masu laifi ne amma sai kawai suka bude musu wuta inda suka kashe mutum 12.

BBC ya ruwaito Ardon yana cewa, mutum hamsin ne suka bata bayan sun guje wa harbe-harben ’yan bindigar, cikinsu har da mata da kananan yara.

Kazalika ’yan bindigar sun tafi da shanu 130.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Usman Abdulahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun kama mutum hudu daga cikin ’yan bindigar.

Tuni dai aka yi jana’izar mutanen da suka mutu.