Gwamnatin Tarayya ta maka kamfanin Facebook a kotu

0
80

Hukumar kula da tallace-tallace ta kasa, ta ce ta shigar da kamfanin Meta mamallakin Facebook da Instagram da WhatsApp da wakilinsa kamfanin AT3 Resources Limited kara a kotu, a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Talata, hukumar ta ce ci gaba da wallafa tallace-tallace ga masu bibiyar Facebook da Instagram a Nijeriya ba tare da tabbatar da samun amincewa kafin fitar da su ba, haramun ne.

Hukumar ta ce kamfanin Meta ya ci gaba da yada irin wadannan tallace-tallace da suka jawo wa gwamnatin tarayya asarar madudan kudade.

Hukumar tana neman kamfanin na Meta ya biya tarar Naira biliyan 30 kan take dokokin tallace-tallace da ya yi.

Hukumar ta ce, kafin yin kowace irin talla a Nijeriya akwai bukatar sahalewa daga gare ta.

Sai dai tace kamfanin na Meta ya yi wa wannan doka hawan kawara.