Ina nan lafiya kuma ashirye nake tsaf na ja ragamar Najeriya – Tinubu

0
96

Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi watsi da jita-jitan da ake cewa jinya ya tafi birnin Landan.

Tinubu ya saki sabon bidiyon da dan tsokaci a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba, 2022.

Bidiyon mai tsayin sakwanni bakwai kacal ya nuna Tnubu yana motsa jiki kan keken tafi da gidanka cikin dakinsa a Landan.

A jawabin da yayi, Tinubu yace:

“Wasu da dama sun ce na mutu; wasu sun ce na janye daga kamfen neman shugaban shugaban kasa.”

“Amma kash! Gaskiyan magana shine ina da karfi ne, ina cikin koshin lafiya kuma shirye nike da bautawa yan Najeriya tun ranar farko.”

Kalli bidiyon;