Putin ya sanar da kammala mayar da yankunan Ukraine 4 mallakin Rasha

0
89

Shugaba Vladimir Putin ya bayyana cewa yankunan Lugansk da Donetsk da Kherson da kuma Zaporizhzhia za su ci gaba da kasancewa wani sashe na Rasha har abada bayan kammala sanya hannu kan dokar da ta mayar da yankunan 4 karkashin Moscow.

A jawabin da ya gabatar yayin bikin mayar da yankunan 4 karkashin ikon Rasha da ya gudana a dakin taro na Georgian, Putin ya bayyana cewa Moscow za ta jibinta lamurran al’ummar yankunan ta hanyar basu cikakkiyar kulawa.

Matakin kwace iko da yankunan 4 dai na zuwa ne bayan zaben raba gardamar ballewar yankunan da ya nuna al’ummominsu sun goyi bayan koma karkashin ikon Rasha.

An dai shafe kusan watanni 8 ana tafka yaki tsakanin Rasha da Ukraine wanda ya kai ga asarar dubunnan sojoji daga dukkanin bangarorin biyu.

Tuni dai kasashen Duniya suka yi kakkausar suka ga matakin na Rasha, inda Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress ke cewa ana rayuwa a zamanin da aka wuce makamancin mulkin mallakar yayinda kungiyar EU ke cewa baza ta zuba ido tana kallon Putin ya mayar da yankunan karkashin Rasha da karfin tuwo ba.