An samu gidan abinci mai karbar Pi a Kano

0
86

Bayan dogon jira da zaman tsammani da masu shiga manhajar Pi sukeyi a Dadin Duniya ,yanzu Yan Pi a Kano sun samu kwarin guiwa sakamakon billar gidan Abinci da ake Bada Pi a karbi abincin da ake so.

Wannan na nuna cewa dogon zaman jira zai iya zuwa karshe musamman a Kano.

Jaridar Hausa 24 ta gano cewa a cikin minti Daya masu cin Abinci zasu tura Pi din domin karbar Abinci a gidan abincin Mai suna Nafagode Dake unguwar Dan Dago a tsakkiyar Birnin Kano.

Alhaji Umar Muhammad Nafagode Wanda shine Mai gidan abincin yace ya kaddamar da wannan cinikayya da Pi ne tun a ranar 25 ga watan Agusta na shekarar 2022.

Yace ya dauki matakin ne domin karfafa guiwar masu yin Minin din Pi a Kano da Kuma kunyata wadanda suke ganin hada hada da Pi din tatsuniya ce.

Zuwa yanzu a Fadin Duniya akwai masu shiga manhajar ta Pi su sama da miliyan 33.