Gwamnatin Edo ta sanya dokar takaita zirga-zirga ta sa’a 24

0
124

Gwamnatin Jihar Edo ta sanya dokar takaita zirga-zirga ta tsawon sa’a 24 a garuruwan Obazagbon zuwa Ogheghe, da ke kusa da kauyen Irhirhi-Arogba-Obazagbon-Ogheghe.

Gwamnatin ta ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis 29 zuwa Juma’a 30 ga watan Satumba da muke ciki.

“Gwamnati na gudanar da aikin tsaro a yankin, kuma tana gargadin al’umma da su kaurace wa titin Obazagbon zuwa Ogheghe daga ranar 29 ga Satumba zuwa 30, don kada su jefa rayuwarsu a hadari.