Raba mata da maza a makarantun sakandare ya haddasa zanga-zanga a Jihar Bauchi

0
90

Daliban makarantun sakandare a halin yanzu suna zanga-zanga a titunan Bauchi kan wata sabuwar doka da gwamnati ta kawo na raba mata da maza a makarantu.

Dalibai sun koma makaranta a hukumance  a sassan jihar kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Mr Aliyu Tilde, ya ce gwamnatin jihar ta kammala shiri don raba dalibai mata da maza a makarantun jihar.

Tilde, yayin jawabin da ya yi wa manema labarai bayan taron majalisar zartarwa na jihar, SEC, a Bauchi, ya ce za a aiwatar da dokar ne a inda aka ga zai yi wu.

Kwamishinan ilimin ya yi bayani cewa an bullo da tsarin ne domin magance tabarbarewar tarbiyya da ya zama ruwan dare tsakanin daliban makarantun sakandare.

A cewarsa, ana fatan makarantu masu zaman kansu da ke jihar za su yi koyi da tsarin su raba maza da mata a makarantunsu, maza su rika zuwa makaranta daya, mata su rika zuwa wata daban.