Mikel Obi ya yi ritaya daga buga wasan ‘kwallon kafa

0
105

Tsohon dan wasan tawagar Super Eagles ta Najeriya, John Mikel Obi, ya sanar da yin ritaya daga sana’ar murza leda.

Mikel Obi ya bayyana hakan ne cikin wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram a Talatar nan.

A cewar sakon, “duk wani abu da ya yi farko zai yi karshe, saboda haka da wannan sana’ata ta buga tamaula a yau ta zo karshe.

“Ina mai waiwaye zuwa tsawon fiye da shekaru 20 da na shafe a sana’ar taka leda, kuma na gamsu dangane da duk wasu nasarori da na iya samu a tsawon wannan lokaci.”

Mikel Obi na daya daga cikin fitattun ’yan wasan da suka bayar da gagarumar gudunmuwa a nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta samu wajen lashe Gasar Zakarun Turai a 2012.

Dan wasan na Najeriya wanda ya koma Chelsea tun yana da shekaru 19 da haihuwa, ya shafe fiye da tsawon shekaru 10 a kungiyar, inda a yanzu gabanin wannan hukunci da yanke, yake buga tamaula da kungiyar Kuwait SC a kasar Kuwait.

Mikel Obi wanda ya shahara da ‘a datse a raba’ kasancewarsa dan wasan tsakiya mai buga lamba takwas ko hudu, ya lashe akalla manyan kofuna 11 a wasanni 372 da ya buga wa Chelsea.

Kofunan da Mikel Obi ya daga a Chelsea sun hada da Firimiyar Ingila biyu, Kofin Kalubale na FA hudu, League Cup biyu, Charity Shield biyu, Gasar Zakarun Turai daya da Gasar Europa daya.