‘Yan sanda sun cafke mutum 3 kan zargin fashi da makami a Abuja

0
88

Rundunar ‘Yansanda reshen birnin tarayya (FCT) ta samu nasarar cafke wasu mutum uku bisa zarginsu da kasancewa kwararrun ‘yan fashi da suka addabi hanyar Gwarinpa da ke Abuja tare da kwato motar da suka sata.

Jami’in watsa labarai na hukumar reshen FCT, DSP Josephine Adeh, ya an samu wannan nasarar ne bayan da suka samu kiran waya daga wajen al’ummar da abun ya shafa inda suke shaida musu cewa a ranar Asabar da safiya wasu ‘yan bindiga sun mamaye yankin domin yin fashi.

Ya ce, bayan samamen da ‘yansanda suka kai, sun cafke uku daga cikin ‘yan tawagar masu fashin tare da kwato mota kirar Mercedes Benz GLK 350 Ash colour mai lamba REG. NO. GWA 740 FM, tare da kwamfutoci, wayoyin salula da wasu muhimman kadarori da suka sata daga hannun jama’a.

DSP Adeh ya ce, “Yan bindiga da yawansu ya kai 19 sun mamaye yankin tsohon Gwarinpa tare da yin fashi ga jama’a hade da kwace musu kayayyaki ciki har da mota Mercedes benz da wasu muhimman kadarori.

“Yansanda sun kama mutum uku masu suna Shetima Abubakar, dan shekara 22; Yakubu Iliya, shekara 22, da kuma Haruna Amadu, 54 dan shekara tare da motar da suka yi fashinta kirar Mercedes Benz GLK 350 da wasu kadarorin da muka kwato.”