Peter Obi ya ziyarci Sarkin Kano 

0
78

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi da abokin takararsa, Yusuf Baba Ahmed, sun ziyarci Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar Asabar.

Ziyarar tasu na zuwa yayin da ake shirin bude kofar yakin neman zaben 2023 a hukumance.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, baya ga Sarkin Kano, ’yan takarar sun kuma ziyarci Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim.

Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa, ziyarar ’yan takarar biyu ba ta da wata nasaba da sha’anin siyasa face jajanta wa Sarakunan dangane da ibtila’in ambaliya da aka fuskanta da kuma rushewar wani gini a kwanan nan.

A bayan nan ne dai aka fuskanci ambaliyar ruwa a birnin Dabo wadda ta yi sanadiyar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Cikin wani sako da Peter Obi ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce sun tattauna kan wasu muhimman al’amura da Sarkin Kano, kama daga gobarar da aka yi a wata kasuwa a jihar da kuma ambaliyar ruwa da aka fuskanta a wasu jihohin Arewacin kasar.

Ana iya tuna cewa, a wani zaben bayyana ra’ayi da aka gudanar a makonnin nan, an yi hasashen Peter Obi ne zai lashe zaben Shugaban Kasa na 2023.