’Yan bindiga sun kashe wasu mutum 13 a kauyen Ruwan Jema da ke Karamar Bukkuyum a Jihar Zamfara.
Wani mazauni kauyen mai suna Usman Lawal ya ce, ’yan bindigar sun fara harbi kan mai uwa da wabi yayin da suka shigo garin ana tsaka da sallar Juma’a.
“Muna cikin Sallah a daidai raka’ar karshe, sai kawai suka fara bude wa jama’a wuta.
“Nan fa kowa ya ranta a na kare domin tsira da ransa, amma an yi rashin sa’a mutum 13 sun riga mu gidan gaskiya.
“Akwai kuma gommai da suka jikkata musamman saboda turmutsutsu da turereniya da aka rika yi a yayin da mutane ke kokarin fitowa daga masallacin.
“’Yan bindigar sun kuma kashe wasu mutanenmu da suka tarar kafin shigowa gari, wadanda sai daga baya muka rika tsinto gawarwakinsu a gonaki.
“Har an yanke cewa za a yi wa mamatan jana’iza da misalin karfe 4 na Yammacin ranar Asabar, amma aka mayar da lokacin zuwa 7 na Yamma kasancewar ana ci gaba da tsinto gawarwaki a cikin jeji.
“Yanzu haka wadanda suka jikkata na samun kulawa a cibiyoyin lafiya a nan Zamfara da kuma wasu a makwabta da ke Jihar Sakkwato,” in ji shi.
Sai dai kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ya ci tura, kasancewar bai amsa kiran wayarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Harin na ranar Juma’a na zuwa ne kasa da makonni uku da wasu ’yan bindiga suka sace mutum 44 a wani masallacin Juma’a a kauyen Zugu da ke Karamar Hukumar.
Sai dai daga bisani ’yan bindigar sun sako mutanen bayan karbar kudin fansa na naira miliyan biyar doriya a kan tara musu gajiya da suka yi ta tsawon kwanaki.
Akwai tazarar kilomita akalla 15 tsakanin kauyen Ruwan Jema da garin Bukkuyum, shelkwatar karamar hukumar wanda a baya bayan nan ya fuskaci hare-haren ’yan ta’adda.
Bayanai sun ce mazauna kauyen sun sha biyan ’yan ta’adda miliyoyin naira a matsayin harajin fita gonankinsu.
AMINIYA.