Wani matashi ya kashe iyayensa a kan kudi

0
88
Wani matashi mai shekara 21 ya kashe mahaifiyarsa da mahaifinsa saboda sun hana shi kudi.

An tsinci gawar dattawan ne bayan sun fara rubewa, da saran adda a jikinsu, a ranar Alhamis a garin Nnewi da ke Jihar Anambra.

An gano gawarwakin ne bayan wari ya addabi makwabta a unguwar Abubor Nnewichi-Nnewi ne suka yi ta neman inda warin ke fitowa.

Aminaya ta samu rahoto cewa matashin yana ta’ammali da miyagun kwayoyi, kuma ya kashe iyayen nasa ne bayan wata takaddama, saboda sun hana shi kudin da ya bukata.

Wanda ya yi wannan aika-aikan dalibin jami’a ne a jihar kuma shi kadai iyayen nasa suka haifa.

Mazauna unguwar Abubor Nnewichi-Nnewi sun yi zargin sai da ya kashe mahaifan nasa sannan ya tsere zuwa inda ba a sani ba kwana uku da suka gabata.

Wani dan unguwar da ya nemi a dakatar sunansa ya ce wanda ake zargin sananne ne a unguwar wajen shan kwayar Mkpurummiri (Methamphetamine).

Kakakin ’yan sandan Jihar Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce saran adda da aka samu a jikin gawarwakin alama ce ta an nuna musu rashin imani.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunarsu ta fara farautar wanda ake zargin.

A cewarsa, an tura lamarin zuwa babban sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin gudanar da zuzzurfan bincike.

 

(AMINIYA)