Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu ya ce sunan Sanata Chimaroke Nnamani da ya bayyana mai lamba 350 a cikin jerin sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zaben mai wakilai 422 an shigar da sunan ne bisa kuskure.
Kwamitin ya fayyace cewa ba Chimaroke Nnamani akayi Shirin sanya ba, fa ce tsohon shugaban majalisar dattawa Ken Nnamani wanda sunan ke kamanceceniya.
Kakakin jam’iyyar, Bayo Onanuga, ya ce abisa kuskure aka rubuta sunan.
Duk da cewa Nnamani awatan da ya gabata ya yabawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, bisa irin kwazo da salon siyasarsa na daukaka matsayinsa, sai dai fa shi bai fice daga jam’iyyar PDP ba.
Ayanzu haka dai Chimaroke Nnamani shine kuma dan takarar sanata a jam’iyyar PDP kuma babban jigo a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
Ken Nnamani dai ya kasance jigo a jam’iyyar APC inda ya yi aiki a kwamitin riko na jam’iyyar kafin rugujewarta a farkon shekarar 2022.
Ya kuma yi aiki a kwamitin tantance shugaban kasa na jam’iyyar kuma yana da kima a jam’iyyar.
Sai dai Onanuga ya ce kuskuren ya faru ne saboda kamanceceniya da sunan yayi, wanda in ba haka ba, ba abinda zai sanya asaka Chimaroke cikin jerin mambobi 422 na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar APC.
Babban Daraktan kwamitin yakin neman Zaben shugaban kasa na jam’iyar APC ya kasance gwamnan Filato Solomon Lalong, yayin da James Falake ke amatsayin sakatare.