An sake samun rushewar gini a Legas

0
157

An sake samu wani gini ya ruguje a kan titin Sonuga, layin Palm a unguwar Mushin a jihar Legas.

Babban Sakatare na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas, Dakta Olufemi Oke-Osanyinyolu, ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma’a.

Ya ce, “Wani gini ya ruguje a Mushin ‘yan mintoci da suka wuce. Ana ci gaba da aikin ceto.”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a iya tabbatar da cewa wani ya makale a cikin ɓaraguzan ginin da ya ruguje ɗin ba.

A ƴan kwanakin nan Legas na shan fama da rugujewar gine-gine da dama, lamarin da ya janyo asarar rayukan wasu mazauna garin.