Har yanzu Shekarau ne dan takarar NNPP a Kano Ta Tsakiya – INEC

0
151

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce har yanzu tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, shi ne dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar NNPP.

Tun ranar 29 ga watan Agusta, 2022, Shekarau ya sauya sheka daga NNPP zuwa Jam’iyyar PDP, amma INEC ta fitar da sunansa a matsayin dan takarar jam’iyyar.

A ranar Talata, 20 ga watan Satumba, 2022 ne hukumar ta fitar da jerin karshe na sunayen ’yan takarar shugaban kasa da Majalisar Dokoki ta Tarayya a babban zaben da za a gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Ganin sunan Shekarau a matsayin dan takarar Kano ta Tsakiya a NNPP — alhali tun lokacin sauya shekararsa ya sanar da jam’iyyar da INEC cewa ya janye daga takararsa — ya janyo ce-ce-ku-ce a fagen siyasa.

Aminiya ta tuntubi INEC kan wannan lamari, inda Kwamishina na Kasa kan Yada Labarai da Wayar da Kai na hukumar, Festus Okoye, ya tababtar mata cewa har yanzu tsohon gwamnan shi ne dan takarar NNPP.

Ya ce, “Jadawalin zaben da muka fitar ranar 26 ga watan Fabrairu, 20202 ya sanya 15 ga watan Yuli, 2022, a matsayin ranar karshe ta janyewa daga takara ko sauya dan takarar Majalisar Dokoki ta Tarayya.

“Shi kuma tsohon gwamnan ba tashi janye takarar tasa ba sai ranar 26 ga watan Agusta, 2022.

“Hakan na nufin har yanzu shi ne dan takarar NNPP kuma sunansa ne zai fito a takardar kada kuri’a a matsayin mai neman kujerar a jam’iyyar.

“Bayan ranar 15 ga Yuli, 2022, ba za a iya asuya dan takara ba, sai idan mutuwa ya yi ko kuma kotu ta bayar da umarni, saboda kofar yin haka ta riga ta rufe,” in ji shi.