Gwamnati ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2023

0
115

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON), ta ce ta fara shirye-shiryen aikin Hajji na 2023 don kauce kura-kuran da suka faru yayin aikin 2022.

NAHCON ta ce ta dauki matakin soma shirye-shiryen nata a kan kari ne domin cim ma nasara yayin Hajjin na badi.

Shugaban hukumar na kasa, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ne ya bayyana haka sa’ilin da yake jawabi a wajen taron lakca da mika lamabar yabo dangane da Hajjin 2022 wanda kafar IHR ta shirya a Abuja.

Hassan wanda ya samu wakilcin Daraktan Gudanarwa na hukumar, Dokta Ibrahim Sodangi, ya ce sun soma shirye-shiryen ne daga lokacin da aka kammala Hajjin 2022 tun kafin ma su baro Saudiyya.

Ya ce tuni NAHCON ta gana da masu ba da masauki don tanada wa ’yan Najeriya masauki mai inganganci yayin Hajjin 2023.

Kazalika, ya ce hukumar na da kudurin shirya babban taro na kasa da kasa domin ganawa da masana daga sassa daban-daban don cim ma nasarar a Hajjin badi.

Daga bisani, Hassan ya yaba wa IHR bisa kokarin da ta yi wajen shirya taron don karrama ma su ruwa-da-tsaki a harkokin Hajji.

Yayin taron, an mika lambobin yabo ga wadanda suka cancanta da suka hada da hukumomin alhazai na wasu jihohi, daidaikun jama’a da sauransu.

Gwamna Aminu Bello Masari  na jihar Katsina da wakilin Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano da wakilin Gwamna  A.A Sule na Jihar Nasarawa, sarakuna, ‘yan siyasa da sauransu na daga cikin wadanda suka halarci taron wanda ya gudana a zauren taro na Babban Masallacin Kasa da ke Abuja a ranar Alhamis.