Kotu ta aike da makashin Ummita gidan gyaran hali

0
152

Kotun Majistare Mai Lanba 30 karkashin jagorancin Mai Sharia Hanif Sanusi Ciroma ta aike da Dan Chana nan zuwa gidan gyaran Hali sakamakon Rashin hurumin da kotun ke dashi.

A zaman kotun na yau Lauyan gwamnati Mai gabatar da Kara Barista Khalifa Auwal Hashim yaroki kotu data mayar da Wanda ake tuhuma gidan gyaran Hali a ajiyeshi har Sai ansami shawarwarin maaikarar Sharia sakamakon cewar kotun batada hurumi

Ana dai zargin Mr.Frank Geng Qwarong da laifin kashe wata mace Mai suna Ummu kulsum Sani inda ake zargin yayi anfani da wata wuka ya hallaka ta.

Kotun ta amince da Rokon Mai gabatar da Kara inda ta maidashi gidan gyaran Hali har zuwa ranar 13/10/2022 domin sake gabatar dashi.