INEC ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa na 2023 da ƴan majalisar dokoki

0
192

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa da majalisar dattawa da kuma na majalisar wakilai na dukkan jam’iyyun ƙasar da za su fafata a zaɓukan 2023.

INEC ta fitar da jerin sunayen ne a ranar Talata, 20 ga watan Satumban 2022, inda ta ce jerin na ƙu she ne da sunayen ƴan takara daga jam’iyyu 18.

An wallafa jerin sunayen na ƴan takara daga dukkan mazaɓun ƙasar a shafin intanet na INEC.

Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisun dokokin tarayya ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 sai na gwamnonin da majalisun dokokin jihohi ranar 11 ga watan Maris din 2023.

A jerin sunayen, akwai ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu 18 daga jam’iyyu daban-daban, sai kuma ƴan takarar majalisun tarayya daga jihohi 36 da babban birnin ƙasar Abuja, ƙarƙashin jam’iyyu daban-daban.
Baya ga sunayen ƴan takarar da ta wallafa, INEC ta kuma bayyana jinsi da shekaru da matakin ilimi na kowane ɗan takara.

INEC

(BBCHAUSA)