Buhari ya jinjinawa NDLEA saboda babban kamun da ta yi na hodar ibilis

0
142

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjinawa shugaban Hukumar NDLEA dake yaki da miyagun kwayoyi, Janar Buba Marwa mai ritaya tare da jamiā€™ansa sakamakon gagarumar nasarar da suka samu wajen kwato kilo 1,8555 na hodar ibilis a birnin Lagos.

Buhari ya jinjinawa Marwa ne lokacin da ya buga masa waya daga Amurka inda yake halartar taron Majalisar Dinkin Duniya saboda rahotan nasarar da hukumarsa ta samu.

Shugaban kasar ya shaidawa Marwa cewar yana matukar farin ciki da kokarin da yake yi a Hukumar wajen kawar da amfani da kuma safarar kwayoyin wadanda ke yiwa jamaā€™a illa.

Sanarwar da mai baiwa shugaban kasar shawara akan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya rabawa manema labarai tace, Buhari ya bayyana cewar yana matukar alfahari da nasarorin da Marwa ke samu, abinda ke nuna cewar bai yi kuskure ba wajen nada shi a matsayin jagoran NDLEA.

Adeshina yace Buhari ya kuma shaidawa tawagar ministocinsa dake tare da shi a New York cewar, Marwa na aiki tukuru, domin kama tan biyu na hodar ibilis ba karamin aiki bane.

A ranar Litinin Hukumar NDLEA ta gabatar da tarin hodar da ta kama wanda aka mata kudi akan dala miliyan 278 ko kuma naira biliyan 193 tare da wasu mutane 5, cikinsu harda wani dan kasar waje da yayi suna wajen hada-hadar kwayar.

Sanarwar tace jamiā€™an Hukumar sun kwashe kwanaki 2 suna aiki a Lagos kafin kama hodar, bayan daukar dogon lokaci suna dana tarko.