‘Yan sanda sun fadada bincike kan dan Chana da ya kashe budurwassa a Kano

0
93

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tace ta samu nasarar cafke wani mutum dan asalin kasar Sin wanda ake zarginsa da laifin hallaka budurwassa ta hanyar sassoka mata wuka a jikinta.

Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan da yammacin yau Asabar.

SP Kiyawa ya ce lamarin ya farune a daren jiya Juma’a a unguwar Jambulo dake nan Kano, inda mutumin mai suna Jang Qrong ya hallaka budurwar tasa mai suna Ummita ta hanyar caccaka mata wuka a jikinta, wanda daga bisani likitoci suka tabbatarda mutuwarta.

Haruna Kiyawa ya ce yanzu haka kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Abubakar Lawan ya bada umarnin dawo da binciken lamarin zuwa babban sashen binciken aikata manyan laifuka domin fadada bincike akai.

Rundunar na shawartar al’umma dasu kara sanya ido a yankunansu domin kama duk wasu batagari domin mika su ga hukumomin tsaron da suka dace.