Mutane miliyan uku suna mutuwa a duk shekara saboda kuskuren ayyukan likitoci – WHO

0
126

Hukumar Lafiya ta majalisar Dunkin duniya WHO tace a duk shekara mutane sama da miliyan Uku suna mutuwa a duniya sakamakon kura kuren da ake samu a bangaren ayyukan likitoci da sauran ma’aikatan Lafiya .

Daraktan hukumar Lafiya ta majalisar Dunkin duniya Mai kula da Nahiyar Afurika Dr Matshidiso Moeti shine ya bayyana Hakan a game da ranar kula da ingancin lafiyar mutanen da suke rashin Lafiya ta duniya.

Taken bikin na bana shine Bada kulawa ga marasa Lafiya yadda ya kamata ,ba tare da cutarwa ba .

Tace anfi samun tabarbarewar bangaren Lafiya lokacin da akasha fama da cutar Covid 19 har zuwa yanzu.

Dr Moeti ta Kara dacewa ,Koma bayan bangaren Lafiya da karancin kwararrun likitoci da da rashin Bada horo da rashin yanayi Mai kyau na aiki a kasashen duniya musamman masu tasowa ,na daga cikin abinda ke janyo samun Kura kurai a aikin duba marasa Lafiya har wasu su rasa rayuka su .

Tace a yanzu haka Babu takamaiman kididdigar mutanan da suke mutuwa a Afurika saboda wannan matsala ,Amma dai matsalar tafi kamari a Nahiyar .

A duk ranar 17 ga watan Satimbar ko wacce shekara Majalisar Dunkin duniya karkashin hukumar Lafiya ta duniya WHO ke bikin ranar mahimmacin Bada kulawa ga marasa Lafiya ta duniya da fadakar da jama’a mahimmacin kulawa dasu .