Gwamnoni za su kafa kamfanin sufurin jiragen sama a Najeriya

0
120

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce gwamnonin yankin Arewa maso Gabas na shirin kafa kamfanin sufurin jiragen sama na kasuwanci a yankin.

Farfesa Zulum wanda ya zama Shugaban kungiyar Gwamnonin jihohin Arewa-maso-Gabas ya bayyana hakan ne yayin bude taron Kungiyar su karo na bakwai.

Zulum ya ce kamfanin sifirin jiragen a yankin zai taimaka wajen fadada harkokin kasuwanci a yankin Arewa maso Gabas bayan shafe shekaru ana fama da matsalar rashin tsaro wadda ya hana yankin ci gaba.

Gwamnan ya kuma yi tir da halin ko in kula da halin rashin gyara hanyoyin Gwamnatin Tarayya a yankin Arewa maso Gabas.