Gwamnatin jihar Nasarawa ta amince da daukar sabbin likitoci guda 37

0
79

Gwamnatin jihar Nasarawa karkashin jagoranci Injiniya Abdullahi Sule ta amince da daukar sabbin likitoci guda 37 domin inganta bangaren Lafiya a jihar.

Gwamna Sule ya amince da Hakan ne lokacin kaddamar da aikin duba Lafiya kyauta a karamar hukumar Nasarawa ta jihar .

Yace daukar matakin ya biyo bayan bukatar gwamnatin jihar na ganin an cike gibin da ake dashi musamman a sabbin cibiyoyin Lafiya da aka Samar da Kuma sabbin asibititoci da aka Gina .

Gwamna Sule ya Kara dacewa jihar na da burin cimma sabbin muradan Karni masu dorewa na SDGs.

Gwamnan yace tun bayan fito da Shirin kula da Lafiya kyauta da gwamnatinsa tayi a jihar ,kananan hukumomi tara sun Amfana da Shirin.

Daga nan yace mutane 819 sun Amfana da aikin tiyata kyauta yayinda Kuma marasa Lafiya 18000 Suma suka Amfana daga bangarori daban daban.