Buhari ya karbi bukatun ASUU

0
92

Wata tawaga ta musamman ta mataimakan shugabannin jami’o’in gwamnatin kasar nan ta roki shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kan ya yi watsi da tsarin da ake yi na babu aiki, babu albashi ga Malam Jami’o’in dake yajin aiki tsawon lokaci.

Tawagar ta mika bukatar ‘yan kungiyar ta ASUU ne yayin wata ganawa da shugaban kasar a fadar sa dake birnin tarayya Abuja.

Wakilan Yan kungiyar ta ASUU, sun kuma yaba wa shugaban kasar bisa tayin da ya yi musu na karin albashi ga ‘yan kungiyar ta ASUU da kashi 23 da digo 5 da kuma kashi 35 cikin 100, inda suka bayyana jin dadinsu bisa la’akari da hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan.

A martaninsa shugaba Buhari, ya yi alkawarin kara tuntubar masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyar kawo karshen yajin aikin na kungiyar ASUU.

Shugaban kwamitin shiga tsakanin ASUU da gwamnatin Tarayya, Nimi Briggs wanda shi ne ya jagoranci shugabannin kungiyar zuwa fadar shugaban kasar, yace da zarar an gyara tsarin sun yi alkawarin cewa malamai za su rama lokacin da aka bata, kuma za a bude makarantu.