Shu’aibu Lawan Kumurci: Babban burina na zama shugaban kasar Najeriya

0
118

Jarumin fim Shu’aibu Lawan Kumurci ya nuna sha’awarsa na son ganin yana jagorantar mutane a matsayin wani shugaba.

Kumurci ya ce yana da burin son ganin ya zama shugaba na kasa baki daya duba ga abubuwan da gani a rayuwa.

Dan wasan ya ce duk da Allah ya yiwa Najeriya baiwa ta arziki da mutane da duk wasu abubuwan more rayuwa, sai ga shi ana rayuwa mai ban tsoro.

Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Shu’aibu Lawan wanda aka fi sani da Kumurci ya bayyana babban burinsa a rayuwa.

A wata hira da ya yi da sashin Hausa na BBC a shirin ‘Daga Bakin Mai ita’, Kumurci ya bayyana cewa burinsa a yanzu shine ya zama wani jagora wato bima’ana shugaba.