Rushewar katangar makaranta ta kashe yara 2 a Legas

0
107
Wasu yara biyu, Samat Saheed da wata yarinya da ba a fayyace sunanta ba, sun rasa rayukansu a lokacin da katangar makarantar Covenant Point Academy ta rufta musu, a titin Ajose da ke unguwar Amukoko a Jihar Legas.
Jaridar PUNCH Metro ta tattaro cewa yarinyar mai shekara 9, ta zo wuce wa ne ta gaban makarantar, inda shi kuma Samat mai shekaru 3 ke wasa a jikin katangar, kusa da shagon mahaifiyarsa a lokacin da ta rushe a kan su.
Wakilim jaridar ya tattaro cewa, a lokacin da katangar ta danne kananan yaran, sai ta danne kan Samat, inda nan take ya mutu, yayin da yarinyar Æ´ar shekara tara ta fita daga hayyacinta, kuma rahotanni sun ce ta mutu jim kadan da faruwar lamarin a asibiti.
Da yake zantawa da manema labarai, wani ganau, Ganiyu Ayeloja, ya ce mazauna garin da lamarin ya faru sun sanar da Æ´an sanda, inda ya ce an kama mai makarantar.
Shi ma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here