Yan Bindiga Sun Yi Wa Ayarin Gwamnan Jihar Abia Kwanton Ɓauna

0
6

 

Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta a kan ayarin Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, da safiyar Talata a kusa da Filin Jirgin Sama na Sam Mbakwe, dake Owerri, Jihar Imo.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kai harin ne tsakanin Umuowa da gadar Ihite, kuma ya jawo ɗan tashin hankali ga mazauna yankin da matafiya. Sai dai lokacin da aka afkawa ayarin, babu Gwamna Otti a cikin ayarin.

Babu rahoton mutuwa ko rauni a harin, duk da cewa an dakatar da zirga-zirga na ɗan lokaci kafin jami’an tsaro su mamaye yankin.

Har yanzu rundunar ‘yan sandan Jihar Imo ba ta fitar da wata takamaiman sanarwa game da harin ba.

A nasa bangaren, Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Abia, Ukoha Njoku, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, tare da tabbatar wa jama’a cewa Gwamna Otti yana cikin koshin lafiya. Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa saurin kai dauki da kuma daidaita al’amura.

Hukuma na ci gaba da bincike domin gano musabbabin harin da kuma wadanda suka aikata shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here