An shiga zulumi a yankin Ungwan Nungu da ke mazaɓar Bokana dake Karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna, bayan da wasu yan bindiga suka sace mutum 11 da suka dawo daga gona a ranar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun tare mutanen ne a kan wata hanyar daji, inda suka kai su zuwa wani wurin da ba a sani ba. Lamarin ya jefa al’umma cikin tsananin damuwa, musamman ma iyalan wadanda aka sace, wadanda suka shafe dare suna cikin tashin hankali.
Wani mazaunin yankin ya ce wasu daga cikin waɗanda aka sace matasa ne da suka je tattara wake. Ya kara da cewa maharan sun fara tare mutum kusan 15, amma wasu sun tsere, yayin da wasu kuma aka sake su ba tare da sharadi ba. Sai dai mutum 11 har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane, inda ake neman kudin fansa na naira miliyan biyar.
A martaninsa kan lamarin, dan majalisar tarayya mai wakiltar Jema’a/Sanga, Hon. Daniel Amos, ya yi Allah-wadai da kai hari kan mutanen gari masu neman rufin asiri.
Ya kuma roki jama’a su kwantar da hankalin su tare da kasancewa masu lura da kan su, yana gargadin cewa duk wani yunkurin daukar doka a hannu na iya dagula lamarin.


